Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya ba da umurnin cimma nasarar yaki da cutar COVID 19 a Wuhan
2020-03-11 16:44:46        cri
Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Wuhan, wurin da cutar ta fi kamari a kasar Sin, don ba da jagoranci ga aikin dakile cutar COVID 19. Inda ya ba da umurni cewa, kamata ya yi a kara zage damtse don cimma nasarar dakile cutar, ya ce: "Babu abin da zai girgiza mu, ba za mu gajiya ba, ko yin kasa a gwiwa."

Bayan shugaba Xi ya jagoranci aikin dakile cutar sau biyu a birnin Beijing, inda karon farko ya isa birnin Wuhan don jagorantar aikin a wurin da cutar ta fi kamari a kasar Sin, saboda haka, wannan na nuna cewa, matakin shugaba na da ma'ana sosai.

Rahotanni na cewa, akwai fagagen da ake kokarin dakile cutar, daya shi ne asibitoci, sauran daya kuma shi ne unguwani, kuma wuraren da shugaba Xi ya duba. Ana iya ganin cewa, daga lokacin da shugaba Xi ya sauka a birnin, nan da nan ya kai ziyara asibitin Huoshenshan don gai da masu aikin jiyya da suke kan gaba wajen yaki da wannan cuta, inda ya yaba musu cewa, "Ina kaunarku matuka a cikin zuciyata." Haka kuma, ya tattauna ta kafar bidiyon hoto da marasa lafiya wadanda ke samun jiyya, don karfafa musu kwarin gwiwar warkewa daga cutar. Dadin dadawa, yayin da shugaba Xi ya kai ziyara wasu unguwani, ya kalli yadda ake gudanar da aikin ba da himma da tabbatar lafiyar al'umma na yau da kullum da matakan kandagarkin cutar da sauransu, tare da nuna godiya ga sadakarwa da kuma gudunmawar da mazauna lardin Hubei musamman ma jama'ar Wuhan suke bayarwa.

Shugaba Xi ya ce, kamata ya yi, a kara hadin kai da tsayawa kan aikin dakile cutar a wannan lokaci mai muhimmanci ba tare da kasala ba. Matakin da ya bayyana karfin hali da wayin kan shugaban. Saboda jagoranci mai karfi da kuma matakai masu inganci da shugaba yake dauka, da mai da hankali sosai kan lafiyar jama'a, Sinawa sun samu nasarar dakile wannan mumunar cutar, cewar wasu manazarta.

A halin yanzu, cutar na yaduwa a duk fadin duniya, kwanan baya, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO ta nuna damuwarta matuka kan yadda wasu kasashe suka gaza mai da hankali da ma rashin kimtsawa tinkarar wannan cuta, musamman Amurka. Bayanai na nuna cewa, ya zuwa karfe 11 na daren jiya Talata, agogon gabashin Amurka a kalla jihohi 37, da yankin Washington D.C na kasar Amurka sun tabbatar da cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya haura 1000, yayin da wasu 31 suka rasu a sanadiyyar annobar.

Ya zuwa yanzu, kasashen duniya na ganin cewa, barkewar cutar ta zama wata babbar jarrabawa ga dukkan kasashen duniya, kana ta baiwa duniya wata dama ta sake nazari da kimanta matakan da kasashe daban-daban suka dauka. Babban darektan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna cewa, ga yadda shugaba Xi ya jagoranci aikin yakar cutar yayin da ya kai ziyarar birnin Beijing, WHO na kira ga shugabanin kasa da kasa da su nuna jagorancinsu da buri a siyasance kan wannan aiki, kamar yadda shugaba Xi Jinping ya nuna. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China