Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shehun malami: Rangadin da Xi Jinping ya kai Wuhan ya nuna imanin kasar Sin kan dakile cutar COVID-19
2020-03-11 13:13:48        cri
Jiya Talata ne, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin koli na rundunonin sojojin kasar, mista Xi Jinping, ya je birnin Wuhan na lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin don duba yadda ake gudanar da ayyukan rigakafi da shawo kan cutar COVID-19. Dangane da batun, Peter Kagwanja, darektan Cibiyar Nazarin Manufofin Afirka ta kasar Kenya ya gaya ma wakilin CMG cewa, ziyarar Shugaba Xi ta nuna wa duniya imanin da kasar Sin ke da shi a kokarin dakile cutar COVID-19, kuma a karshe kasar Sin za ta sami babbar nasara wajen yakar cutar.

A halin yanzu, an samu bullar cutar COVID-19 a cikin kasashe sama da 100 na duniya. Kagwanja ya ce, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan da suka dace na dakile yaduwar cutar, wadanda suka samar da makoma mai haske ba kawai ga kasar Sin ba, har ma ga duniya baki daya. Ya kuma ce wani abu mai muhimmanci da aka koya daga aikin dakile cutar da ake gudanarwa a kasar Sin, shi ne dole ne a dauki kwararan matakan kandagarki da killacewa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China