Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kudin da kasar Sin ta samu daga bangaren yawon bude ido ya kai fiye da Yuan triliyan 6.6 a bara
2020-03-11 13:08:28        cri

Kwalejin nazarin harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin, ta ce a shekarar bara, yawan mutanen da suka yi yawon shakatawa a gida ko a kasashen waje, duka ya samu karuwa.

Wani rahoto da kwalejin ta fitar a jiya, ya ce a shekarar 2019, yawan mutanen da suka bude ido a cikin kasar, ya kai fiye da biliyan 6, wanda ya karu da kashi 8.4 cikin dari bisa na makamancin lokaci a shekarar 2018, kana yawan kudin da aka samu a wannan fanni ya zarce RMB yaun triliyan 6.6, wanda ya karu da kashi 11 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar 2018.

Ban da wannan kuma, yawan Sinawa da suka ziyarci yankunan ketare ya kai miliyan 155, adadin da ya karu da kashi 3.3 cikin dari bisa na makamancin lokaci na 2018, kuma yawan baki daga ketare da suka yi yawon shakatawa a kasar Sin, ya kai miliyan 145, wanda ya karu da kashi 2.9 cikin dari bisa na 2018. Daga cikinsu, yawan 'yan Asiya da suka yi yawon bude ido a kasar Sin ya kai kashi 75.9 cikin dari, yayin da adadin Turawa ya kai kashi 13.2 cikin dari. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China