Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Malama Yang Mei da ta dukufa a kan noman ganyen shayi da sarrafa su
2020-03-13 12:09:16        cri

 

 

 

 

 

 

 

 

Malama Yang Mei ke nan 'yar shekaru 39 da haihuwa, wadda take rayuwa a gundumar Danzhai da ke yanki mai cin gashin kansa na kabilar Miao da ta Dong da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou na kasar Sin. Malamar ta gama karatun jami'a a shekarar 2000, daga bisani ta koma garinsu, inda ta bi mahaifinta wajen noman ganyen shayi da kuma sarrafa shayi, har ma bisa ga tallafin da iyalanta suka samar mata, ta kafa gonakin shayi da fadinsu ya kai kimanin eka 13. A shekarar 2008, ta kuma kafa kamfaninta da ke gudanar da harkokin noman ganyen shayi, da sarrafa su da kuma sayar da su.

Yau shekaru kusan 20 ke nan, gonakinta sun karu zuwa sama da eka 130, ma'aikatan kamfanin ma sun karu daga 80 zuwa sama da 1000, ciki har da wadanda ke fama da talauci, kuma ta hanyar daukarsu aiki ne aka taimaka musu wajen kara samun kudin shiga.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China