Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An ceto mutane 62 daga Otel da ya rufta a birnin Quanzhou na Sin
2020-03-10 13:09:42        cri

Da misalin karfe 11 da safen ranar 10 ga wata, kungiyar kwana-kwana ta kasar Sin, ta ceto mutane biyu daga otel da ya rufta a ran 7 ga watan a birnin Quanzhou na lardin Fujian dake gabashin kasar Sin. Bayan aikin ceto da ya shafe sama da awo'i 60, an ceci mutane 62 daga wurin, yayin da mutane 20 suka rasa rayukansu. Baya ga haka, akwai sauran mutane 9 da ba a gano su ba, kuma a halin yanzu, ana ci gaba da aikin ceto ba dare ba rana.

Ya zuwa yanzu, hukumar kula da agajin gaggawa ta kasar Sin, ta umurci kungiyar kwana-kwana ta lardin Fujian da wasu magina kimanin dubu daya, da su aiwatar da aikin ceton. Kuma akwai masu aikin sa kai sama da 370 da suka shiga wannan aikin ceto. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China