Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kaddamar da sabbin dabarun yaki da fatara
2020-03-09 11:48:33        cri
Gwamantin kasar Sin ta kaddamar da muhimman matakan da zasu karfafa shirinta na yaki da fatara ta hanyar tallafawa mutanen dake cikin yanayin tsananin bukata, ma'aikatar kula da walwalar jama'a ta kasar ce ta sanar da hakan.

Ma'aikatar ta sanar a lokacin wani taro game da yaki da fatara cewa, za'a gudanar da kidaya domin tantance hakikanin mutanen dake fama da talauci don ganin an bada taimakon ga mutanen da suka cancanta domin su ci gajiyar shirin tallafin da gwamnatin ta bullo da shi.

Sanarwar tace, za'a yi dukkan abin da ya dace don tallafawa runkunin mutane masu karamin karfi, da suka hada da tsofaffi, da kananan yara da masu nakasa wadanda ba zasu iya yin aiki ba, kuma basu da hanyoyin samun kudaden shiga, kana ba su da mutanen da zasu dogara dasu don tallafa musu.

Ma'aikatar ta kuma bada kwarin gwiwa ga kungiyoyin tallafawa al'umma dasu shiga a dama dasu a cikin shirin yaki da fatara kuma su kara azama wajen aiwatar da shirye shiryen da zasu tallafawa al'umma da nufin kawar da fatara a tsakanin jama'a.

Za'a samar da tallafin ne a yankunan da suka fi fama da talauci, a cewar ma'aikatar, inda ta bukaci a samar da karin shirye shiryen bada tallafi, da taimakon kudade da kuma bayar da horo ga yankuna dake fama da fatarar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China