Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kai harin kunar-bakin-wake a kusa da ofishin jakadancin Amurka dake Tunisiya
2020-03-07 17:03:22        cri

 

An kai wani harin kunar-bakin-wake kusa da ofishin jakadancin Amurka dake kasar Tunisiya a birnin Tunis, a jiya Jumma'a, lamarin da ya raunata mutane da dama.

Gidan talabijin na kasar Tunisiya ya ruwaito wata majiya daga bangaren tsaron kasar na cewa, da safiyar jiya Jumma'a, wasu 'yan kunar-bakin-wake biyu a kan babur, sun je wani shingen bincike dake kusa da ofishin jakadancin Amurka don kaddamar da harin, lamarin da ya yi ajalinsu nan take.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China