Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana damuwa game da rikicin bayan zabe a Guinea Bissau
2020-03-06 10:10:45        cri
Kwamitin sulhu na MDD, ya bayyana damuwa dangane da rikicin bayan zabe a Guinea Bissau, biyo bayan zaben da aka yi a watan Disamba, da ya gurgunta tsarin siyasar kasar.

Cikin wata sanarwa, mambobin kwamitin sun yi kira ga jam'iyyun siyasar kasar su mutunta kundin tsarin mulki da tsarin siyasa, domin warware rikicin bayan zaben.

Sun kuma yi kira ga jam'iyyun su rugumi tattaunawa da warware rikicin cikin ruwan sanyi tare da kaucewa dukkan wani abu ko furucin da zai kara ta'azzara lamarin.

An samu tasgaro a tsarin siyasar kasar ne tun bayan zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a watan Disamba, inda hukumar zabe ta kasar ta sanar da shugaban Jam'iyyar adawa, Umaro Sissoco Embalo a matsayin wanda ya doke Domingos Simoes Pereira, na jam'iyyar PAIGC da ta dade tana mulkin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China