Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda ake tabbatar da isassun abinci ga al'ummar birnin Wuhan
2020-03-04 14:37:47        cri

Birnin Wuhan shi ne wuri ne da cutar numfashi ta COVID-19 ta fi kamari, domin magance yaduwar annobar, a ranar 23 ga watan Janairu, aka killace wannan birni mai kunshe da yawan al'umma sama da miliyan 9. Ya zuwa yanzu, sama da wata guda ke nan, a cikin wannan wata, ko kun san ta yadda ake samar da isassun abinci ga al'ummomin birnin?

Odojin abinci guda dubu 130 cikin yini guda

A taron manema labaran da ofishin aikin kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 na gwamnatin kasar Sin ya kira a ranar 26 ga watan Fabrairu, an ce, shugaban sashen ba da hidima da ciniki na ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin Xian Guoyi ya taba bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Fabrairu, an sami odojin abinci guda dubu 130 daga al'ummomin birnin Wuhan.

Oda daya da ta hada unguwanni guda 15 tare

Ban da yin odar abinci kuma, galibin al'ummar birnin Wuhan suna dafa abinci da kansu a gida. Amma ta yaya za su iya samun isassun kayan abinci?

A nan muna da wata taswirar da ta nuna unguwanni guda 15.

An hada wadannan unguwanni guda 15 da wata oda guda daya. A kowace rana, shugaban kamfanin kayan lambu na Lvshuyuan yana samun oda daga al'ummomin unguwannin, sa'annan, ya kai kayan lambu ga wadannan unguwanni guda 15.

Ya zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu, gaba daya akwai kamfanonin kayan lambu guda 16 da suka yi hadin gwiwa da unguwanni guda 180, domin samar musu kayan lambu.

Ana samun kayan lambu daga wurare daban daban na kasar Sin

Hakika akwai wuya wajen samar da isassun abinci ga mutane miliyan 9 cikin kowace rana.

Shi ya sa, daga ranar 23 ga watan Janairu, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fara yin shawarwari da lardin Shandong, da lardin Anhui da sauran larduna guda 6 domin kafa wani tsarin hadin gwiwar samar da kayayyaki a tsakaninsu da lardin Hubei. Kuma ya zuwa ranar 19 ga wata, gaba daya wadannan lardunan 8 sun samar da kayan lambu da 'yayan itatuwa har ton dubu 21 ga lardin Hubei. (Mai Fassarawa: Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China