Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amfani Da Harshen Gado: Kowa Ya Bar Gida, Gida Ya Bar Shi (II)
2020-03-03 14:19:36        cri

A makon da ya gabata mun yi shimfida a kan Harshen Gado a fadin duniya, sannan daga bisani muka kawo wasu matsaloli da suke bukatar magancewa a matakin farko. A yau kuma za mu waiwayi mataki ne na kasa, kana daga bisani mu dire da yadda ake wa Harshen Hausa rikon sakainar-kashi a makaratun sakandare musamman masu zaman kansu.

A daukacin Jihohin Nijeriya, Jihar Adamawa ita ce ta fi kowacce yawan yaruka inda aka tabbatar da cewa tana da yaruka sun fi guda 50.

A wani shiri na Labaru da Al'amuran Yau da Kullum da Gidan Talabijin na Kasa (NTA) ya gabatar a ranar Asabar ta makon jiya, masana da dama sun bukaci a fitar da manufa ta musamman da za a yi aiki da ita a kasa dangane da amfani da harsunanmu na gida.

Musamman wata Farfesa a kan Harshe da aka gayyata a shirfin domin fashin baki daga Jami'ar Ibadan, Farfesa Adenike Akinjobi, ta koka da cewa, ba a bai wa sha'anin Harsunanmu na Gado muhimmancin da ya kamata, shi ya sa mahukuntan kasa suka yi biris da tsara manufofin da za su rika bunkasa harsunan.

Ta buga misali da cewa, idan aka dubi Kasar Faransa, ta yi wa harshenta na Faransanci kyakkyawan tsari (ni kuma zan kara da Harshen Sinawa, Mandarin) na kiyaye shi da bunkasa shi, don haka ta bayar da shawarar a zo da wasu tsare-tsare da za su bunkasa Harsunanmu na Gado. Daga cikin tsare-tsaren a sanya batun karfafa amfani da harsunan a makarantu maimakon dankwafar da su har a ce za a rika hukunta yaro idan ya yi magana da yarensa na asali a makaranta.

Haka nan sauran masanan da aka ji ta bakinsu a rahotannin da aka gabatar a cikin shirin su nemi a kara yawan malaman da za su rika koyar da nazarin Harsunan Gado a kanana da manyan makarantunmu

A wani rubutu da ya yi domin bikin ranar Harshen Gado na shekarar 2020, Dafta Ganiu Abisoye Bamgbose, ya yi bayanin cewa a kokarin wasu iyayen na mayar da harshen da za a rika magana da shi a gidajensu ya zama Ingilishi zalla, sai suka bata saka, inda yaran ke shirin tashi ba-su-ga-tsuntsu-ba-su-ga-tarko. "Abin kyama ne ma a wasu gidajen a rika magana da Harshen Gado, a karshe sai mu samu tsatson da ba su iya Harshensu na Gado kamar yadda ya kamata ba, kuma ba su iya Harshen na Aro da kyau ba. Irin hakan kan haifar da rikicewar amfani da harsunanmu na iyaye da kakanni da kuma na Ingilishin da muka ara muka yafa".

Bayan Malamin ya kawo wasu misalai na yadda ake cakudi wurin gauraya Harsunanmu na Gado da na Aro ba tare da an tsaya an kwarance wa daya ba kamar yadda ya kamata, ya ba da shawarar cewa ya kamata iyaye su mayar da hankali wajen koya wa 'ya'yansu Harshensu na Gado da al'adun da aka gada da farko, domin rigakafin kashe harshen nasu murus ko kawar da shi daga doron kasa da kuma kiyaye bata wa Malam Mai Jajayen Kunnuwa harshensa da ya kuke wajen mallaka duniya da shi. Duk da haka, Dafta Ganiyu ya ce matukar an bi tsarin da ya kamata, mutum yana iya zama gwani wurin magana da harsuna biyu ko fiye da haka a duniya bayan nasa na asali.

Wakazalika, a wata mukala da ya rubuta da Harshen Ingilishi a Jaridar New Nigeria, wani marubuci, Malam Auwal Ahmed Ibrahim Goronyo, ya bayyana cewa masu bincike na ilimi sun gano cewa Harsunan Gado su ne mafi tasiri da fahimtar da dalibai karatu a makarantu, kuma a kan haka ne a shekarar 2017, Ministan Kimiyya da Fasaha na Nijeriya, Ogbonnaya Onu ya sanar da cewa, Gwamnatin Tarayya ta yi shirin fara koyar da Darussan Lissafi da Kimiyya da Harsunan Gado. Amma har yanzu ba a gani-a-kasa ba.

Don haka, marubucin ya nemi gwamnatin ta yi la'akari da alfanun karantarwa da Harsunan Gado kamar yadda wasu kasashen Afirka suka yi tare da gaggauta fara aiwatarwa.

Har ila yau, a wani bincike da ya gabatar game da yanayin koyar da Hausa a manyan makarantun sakandare, wani Malamin Hausa, Malam Is'haq Idris Guibi, ya bayyana takaici a kan yadda ake wa abin rikon sakainar-kashi musamman a makarantu masu zaman kansu wadanda kusan za a iya cewa sun cika ko ina a sassan Arewa.

Binciken wanda ya kuma gabatarwa a shekarar 2013, ya fara da bayyana cewa, "Harshen Hausa na daya daga cikin manyan Harsuna da ake amfani da su, ba a Afirka kadai ba, har ma a kasashen da suke tinkaho a yau cewa su ne masu fada a ji a duk duniya. A kokarin Nijeriya na kamo sahun wadannan kasashe masu tinkahon fada a ji ne, wato ta fannin siyasa, da kimiyyya da fasaha, sannan uwa-uba, ta fannin tattalin arziki, ya sa aka tilasta wa dalibai koyon manyan harsunanmu na kasa, wato Hausa da Ibo, da Yarbanci, a kwalejojinmu, da makarantunmu na sakandare, tun ba ma kwalejojin tarayya ba. Domin duk kwalejin gwamnatin tarayya da ka zaga a kasar a yau, za ka tarar cewa akwai kwararrun malaman nan uku da aka tanada don koyar da harsunan namu uku na kasa. Su kuma dalibai, in an ce yaro gaba da baya bahaushe ne, za a tilasta masa, ya koyi Hausa, sannan ya koyi ko dai harshen Ibo, ko Yarbanci. Kazalika, idan yaro gaba da bayansa dan Ibo ne, za a tilasta masa, ya koyi Ibo, da ko Hausa, ko ya hada Ibo da Yarbanci. Haka ma dan Bayarabe, dole ne ya koyi yadda ake nazarin Yarbanci, da ko Hausa, ko ya hada Yarbanci da Ibo. Sannan kowanne yana da Manhajarsa daban. Misali Manhajar da za ka yi amfani da ita wajen koya wa wanda, gaba da bayansa, bahaushe ne, daban da wanda za ka koya wa dan bayerabe, ko dan Inyamuri wato Ibo, da ba su san ko zo in kashe ka ba a Hausa.

"Idan ka leka makarantun sakandare masu zaman kansu da ke Arewacin kasar nan kuwa, za ka tarar da cewa akwai Malamin Hausa ne kawai kwaya daya tal. Irin wadannan makarantun, za ka tarar cewa in ma akwai 'ya'yan Hausawan, to fa 'yan kalilan ne. Saboda haka, maimakon a bar malamin Hausan ya bi tsarin da na zayyana a baya, wato irin tsarin kwalejojin gwamnatin tarayya, sai a ce wa Malamin ya dauka kowanne yaro gaba da bayansa bahaushe ne. Saboda haka, Malamin ya yi amfani da Manhajar da ake koya wa wanda ya san zo in kashe ka. A saboda haka sai Malamin ya kwashe shekaru yana koya ma yara wanda a karshe, ka samu cewa yaran ba su san inda aka nufa ba. A yi jarabawa, a karshe duk yaran su zube. Ka ga ba laifin iyaye ba, ba laifin Malami ba, kuma ba laifin yaro. Sannan ba dan karamin wulakanci ake nuna wa Malaman Hausa a irin wadannan makarantu ba. Ga mai son saninsu ga 'yan misalai. Na farko kai Malamin Hausa, kai kadai za a danka wa tun daga 'yan aji daya, har zuwa 'yan aji shida, wai da sunan ka koya musu Hausa. Ga jakin Kano ya iso. Abu na biyu, sai ka koya wa yaro Hausa tun yana aji daya, sai ya kai aji hudu, sai ya kira babansa da sunan cewa shi fa, ya gaji da Hausar. Wani lokaci makarantar ce ke ba da umarni bayan ka koyar da yaron gaba da bayansa bahaushe ne wato tun daga aji daya, har aji shidansa, sai a kawo umarnin cewa in ya ga dama ya rubuta ta a jarabawarsa ta fita. In bai ga dama ba, ya watsar da Hausar. Wani abin ban haushi, shi ne irin wadannan Malaman Hausa, su ake biya albashi dan kankani wai saboda darajar mai koyar da Hausa ba ta kai ta masu koyar da sauran fannonin ba. Sannan har ila yau, da gangan in an zo shirya jarabawa a irin wadannan makarantu, sai a sa jarabawar Hausa a karashe wato bayan an gama kowacce jarabawa, sai a ce ai keken rubutu ya lalace, ko kuma an buga jarabawar Hausar, amma kafin a bai wa yara su zana jarabawar, sai a nemi taimaka wa dalibai satar jarabawa. Idan Malami ya ki ba da hadin kai, a buga masa sharri a kore shi. Wata matsalar kuma da Hausa ke fuskanta a irin wadannan makarantun masu zaman kansu, ita ce idan an zo bikin yaye dalibai duk yara da suka yi fice a fannin harshen Hausa, sai a kudundune kyautar da za a ba su a cikin takardar kunshe kosai da tsire, amma sauran fannonin sai a sami leda mai tsada da kyalli a kudundune kyautar a ciki a ba su. In ana kara wa malamai girma kuwa, sai a ki kara wa Malamin Hausa. Saboda wai in ana maganar malamai, shi ai ba zai tsoma baki ba. Wai mene ne ke da wuya a cikin Hausar? Magana ta karshe ita ce in aka kasa makarantun da ke zaman kansu a kasar nan, cikin kashi goma, kashi biyu ne kawai suke daukar malaman Hausa don koyar da Hausar. Kai malamin Hausa, ko ka cusa kanka cikin irin wadannan makarantu, tursasawa ya sa ka bar wajen,".

Malam Guibi ya kawo shawarar cewa, "ya kamata, daukar malaman da za su koyar da wadannan harsunan namu uku, ta zama sharadi na farko kafin a ba da izinin bude irin wadannan makarantu masu zaman kansu. Kuma ya kamata ma'aikatar ilimi, ta cire kunya, ta dinga sa ido a kan irin wadannan makarantu. Don kuwa akwai irin wainar da ake yawan toyawa da ba su lissafatuwa".

Da fatan mahukuntan da abin ya shafa za su yi la'akari da wadannan shawarwari na masana tare da aiwatar da su domin raya harsunan namu da muka gada tun iyaye da kakanni, ko ma dan kar mu fada sahun wadanda ake nunawa ana musu dariyar 'kowa ya bar gida, gida ya bar shi'.(By Abdulrazaq Yahuza)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China