Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yabawa namijin kokarin kasar Sin wajen yaki da COVID-19
2020-03-03 10:48:50        cri

Wani kwararre kan harkar tsaro dan kasar Tunisia, Badra Gaaloul, ya ce kasarsa na goyon bayan kasar Sin da al'ummarta a yakin da suke da cutar numfashi ta COVID-19.

Badra Gaaloul, wanda shi ne shugaban cibiyar nazarin dabarun tsaro da ayyukan soji na Tunisia, ya shaidawa Xinhua cewa, duk da mummunan tasirin cutar kan tattalin arzikin kasar Sin, a shirye kasar take ta shawo kan matsalar la'akari da yadda ta nuna karfinta na tunkarar manyan kalubale a baya.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta kuma yi amfani da yawan al'ummarta da kuma kudi, wajen taimakawa kasashe da dama da annobar ta shafa. Yana mai cewa, wannan ya nuna irin karfin da kasar Sin ke da shi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China