Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump:Kasar Sin ta taka rawar gani wajen shawo kan cutar numfashi ta COVID-19
2020-03-01 17:20:50        cri
A jiya Asabar, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kira taron manema labarai a fadar White House, inda ya jinjinawa kasar Sin kan nasarorin da ta cimma wajen shawo kan cutar numfashi ta Covid-19.

A yayin da ya amsa tambayar wakilin gidan talabijin na CCTV game da ko gwamnatin Amurka zata dauki matakai makamancin na kasar Sin idan yanayin cutar ya tabarbare a kasar, ya ce, kasar Sin ta samu gagarumar nasara wajen dakile cutar, kuma Amurka a halin yanzu na tunani kan daukar wasu matakan da Sin ta dauka.

Ya kara da cewa, kasashen biyu na ci gaba da tuntubar juna, ciki har da shugaban kasar Sin Xi Jinping da ma shi kansa. Ya kuma yi fatan za a ga bayan cutar tun da wuri, shi ya sa yake kokarin daukar matakai. Kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba, kuma mun lura da cewa, tuni har kamfanin Starbucks ya dawo bakin aikinsa. Baya ga haka, kamfanin Apple ma ya dawo da ayyukansa a kasar Sin daga dukkan fannoni. Da gaske ne kasar Sin ta taka rawar gani wajen shawo kan cutar.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China