Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Yaya kasar Sin ta kashe kudin dakile cutar COVID-19?
2020-02-29 21:21:33        cri

Zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta riga ta ware kudin Sin Yuan biliyan 25.29 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.6) don tallafawa aikin dakile yaduwar cutar COVID-19, yayin da kananan hukumomin wurare daban daban na kasar suka ware Yuan biliyan 64.86 (dalar Amurka biliyan 9.3). Wato baki daya hukumar kasar ta ware kudin da ya zarce Yuan biliyan 90 (dalar Amurka 12.9) wajen gudanar da aikin tinkarar annobar COVID-19.

Ta yaya ake amfani da kasafin kudin?

Idan muka dauki lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin a matsayin misali. Zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu, hukumomi na matakai daban daban na lardin sun ware kudin da yawansa ya kai biliyan 4.4 (dalar Amurka miliyan 629) don taimakawa aikin hana yaduwar cutar COVID-19.

Ta yaya aka yi amfani da kudin rance?

Wannan hoto ya nuna matakin da aka dauka a birnin Nanjing, hedkwatar lardin Jiangsu, inda a ranar 29 ga watan Janairun da ya gabata, hukumar birnin ta ware Yuan miliyan 50 don taimakawa kamfanonin hada magunguna don su samar da nau'rorin kariya, da kuma magunguna. Sa'an nan a birnin Lian'yun'gang, duk a lardin Jiangsu, tun daga farkon watan Fabrairu, an samar da kudin tallafi Yuan miliyan 1.2 ga matalauta, da marayu, da nakasassu.

Ta wadannan misalai, za a iya ganin cewa, tun da kudin gwamnati daga jama'a ne ake samu, yanzu ana amfani da kudin don taimakawa jama'a, da ba su kariya yayin da ake fama da barazanar cuta.

Wane ne ke samun kudin rance daga bankuna?

Rancen da bankunan kasar Sin suka samar yana taimakawa ayyuka guda 2, wato dakile yaduwar cuta, da farfado da ayyuka.

A lardin Guangdong da ake samun ci gaban tattalin arziki, tun daga ranar 25 ga watan Jainairu har zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu, bankunan dake waje da birnin Shenzhen sun samar da rancen kudi da ya kai Yuan biliyan 60. Mun san a lardin Guangdong akwai masana'antu da yawa, cikinsu akwai masu samar da kayayyaki, da masu kula da ciniki da kasashe waje. A wannan karo, an ba da rancen kudin da ya zarce Yuan biliyan 12.2 don tallafawa sana'o'in sayar da kaya, sa'an nan an ware rancen kudin da ya kai Yuan biliyan 7.6 don taimakawa ayyukan zirga-zirgar motoci da sufuri, da ajiye kayayyaki, da jigilar kaya, dukkansu sun kasance ayyukan da ake tsananin bukatar maido da su cikin sauri don biyan bukatun dakile yaduwar cutar COVID-19.

Ban da wannan kuma, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta sanar a kwanakin baya cewa, ana kokarin samar da kudin da ake bukata don gudanar da ayyuka dakile cutar COVID-19, kana ana ba da kudi don tallafawa aikin samar da kayayyakin da ake bukata. Sa'an nan ana kokarin kawar da illolin da annobar ke haifarwa tattalin arzikin kasar Sin. A nan gaba, za a kara kyautata dabara don hana yaduwar cutar COVID-19, tare da ciyar da tattalin arziki da zaman al'ummar kasar gaba.

A ganin wasu manazarta harkokin tattalin arziki, yadda ake samar da makudan kudi don tallafawa ayyuka daban daban a lokacin da ake kokarin dakile cuta a kasar Sin, gami da managartan manufofin kudi da aka samar a kasar, suna taka muhimmiyar rawa wajen kwantar da hankalin jama'a, da karfafa gwiwar kamfanoni. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China