Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Masu Son Ganin "Rushewar Kasar Sin" Ba Su Cimma Burinsu Ba
2020-02-29 21:10:42        cri

A shekaru gomai da suka wuce, wasu manazarta al'amuran duniya da kafofin yada labaru na kasashen yamma sun yi ta hasashen samun "rushewar kasar Sin" a lokuta daban daban. Bayan bullar cutar COVID-19 a wanna karo, sun kwatanta annobar da bala'in burbushin nukiliya da ya abku a Chernobyl a lokacin tarayyar Sobiet USSR, inda suka ce annobar da ta abku a wannan karo zai sa kasar Sin ta rushe. Amma za su yi bakin ciki, ganin yadda kasar Sin ta samu nasara a kokarinta na dakile cutar.

Zuwa ranar 28 ga wata, yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Sin, ban da lardin Hubei, adadin ya ragu zuwa 4, yayin da kamfanoni na wurare daban daban na kasar ke kokarin farfado da ayyukansu. Duk a wannan rana, an gabatar da wani rahoto game da binciken da tawagar hadaddiyar kwararrun hukumar lafiya ta duniya WHO da na kasar Sin ta yi kan annobar COVID-19, inda aka nuna cewa, kasar Sin ta yi nasara wajen toshe hanyar bazuwar cutar, ta yadda ta samar da fasahohi da dabaru masu muhimmanci ga sauran sassan duniya ta fuskar dakile cutar COVID-19.

Wannan rahoton ya bata ran wadanda ke hasashen ganin "rushewar kasar Sin". Inda gidan rediyon kasar Australiya ABC ya wallafa wani bayani kan shafinsa na Intanet a ranar 27 ga wata, cewa: Idan a karshe dai jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta koya mana wani darassi, to yaya za a yi? A lokacin za mu tambayi kanmu, ko za mu iya shawo kan yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri kamar yadda aka yi a kasar Sin?

Hakika daidai kamar yadda aka rubuta a cikin bayanin kamfanin ABC, ta la'akari da matakan da aka dauka a kasar Sin, misali, dukkan bangarorin kasar sun zama a karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da yadda aka kafa wani asibiti na musamman don jinyar masu kamuwa da cutar COVID-19 a birnin Wuhan cikin kwanaki 10, da tsaurarran matakan hana yaduwar cutar da ba a taba ganin irinsu ba a tarihin kasar Sin, to, za a iya ganin yadda tsarin siyasar kasar ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da wasu managartan matakai.

Kwayoyin cuta ba su san bambancin kasashe, da kabilu ba, balle tsarin siyasa, don haka cutar COVID-19 ita ma tana haifar da barazana ga tsarin dumokuradiya irin na kasashen yamma. Duk da cewa, jaridar "The New York Times" ta ce wai "ba za a killace wani birni a kasar dake da dimokuradiya ba", amma a hakika kasar Italiya ta riga ta fara daukar dabarar "salon Wuhan" a kwanakin baya, inda ta killace wasu biranen da aka fi samun bullar annobar.

Yadda ake kallon annoba a matsayin batun siyasa, da kokarin shafawa kasar Sin bakin fenti, ba za su taimaka ga yunkurin hana yaduwar cuta ba, maimakon haka, za su sa lalata damar shawo kan annoba. Ya kamata a daina nuna bambancin ra'ayin siyasa, maimakon haka a dauki ra'ayi na girmama kimiyya da fasaha, da kokarin koyon fasahohin sauran mutane, da hadin gwiwa, domin ta haka ne kadai za a iya samun damar hana yaduwar cutar COVID-19 a duniyarmu. (Mai Fassarawa: Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China