Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Ana kokarin samar da allurar rigakafin cutar COVID-19
2020-02-29 21:06:01        cri

Babban magatakardan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Ghebreyesus, ya bayyana jiya a birnin Geneva na kasar Switzerland cewa, yanzu haka ana kokarin nazari kan allurar rigakafin cutar COVID-19 na nau'ika fiye da 20, sa'an nan wasu daga ciki an riga an fara gwajinsu kan majiyyata, don haka ana kyautata zaton samun sakamako na farko cikin wasu makwanni.

Ghebreyesus ya kara da cewa, ko da yake annobar na bazuwa a wurare daban daban a duniya, amma fasahohin da kasar Sin ta samu sun shaida cewa, sai na dauki kwararran matakai, da gano wadanda suka kamu da cutar tun da wuri, sa'an nan a killace wadannan mutane don kula da lafiyarsu, gami da sa ido kan wadanda suka taba mu'ammala da masu cutar, sannan za a samu damar hana cutar ci gaba da bazuwa, ta yadda ba za ta gama gari ba. Ghebreyesus ya ce, babban abokin gaba da ake fuskanta ba kwayoyin cuta ba ne, tsoro ne, da jita-jita, gami da yunkurin shafa wa wani kashin kaza. A cewarsa, abin da ake bukata yanzu shi ne gaskiya, da sanin ya kamata, gami da hadin gwiwa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China