Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar tsaron kasar Sin: Ba wanda ke iya hana tasowar kasar
2020-02-29 17:20:30        cri

Ministan tsaron Amurka, Mark Esper, ya bayyana a kwanakin baya cewa wai "kasar Sin na neman samun karfin soja don shirya kai hari ga wasu kasashe". Dangane da wannan zance ne, Wu Qian, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin, ya bayyana wa maneman labaru a jiya Jumma'a cewa, maganar Esper karya ce, kuma ba wanda zai iya hana ci gaban kasar Sin.

A cewar Wu Qian, kasar Sin tana kokarin aiki da sauran kasashe makwabtanta don daidaita batun da ya shafi yankin tekun kudancin kasar, inda a sannu a hankali ake samun ci gaba a wannan fanni. Amma Amurka, saboda son ranta, tana ta kokarin ta da rikici a yankin, inda take tura jiragen sama da na ruwa na yaki zuwa yankin tekun don nuna fin karfi, ban da haka, tana hada gwiwa da wasu kasashe wajen gudanar da atisayen soja a wannan yanki. Wadannan lamuran sun nuna cewa, Amurka ce dalilin da ya sa ake ta samun aikace-aikacen soja da rikici a yankin tekun dake kudancin kasar Sin.

Sa'an nan, Amurka na neman yin babakere a fannin sararin sama, inda ta kafa rundunar sararin sama, da fara wata gasar na'urorin yaki a sararin samaniya bisa radin kanta. Ya ce hakika Amurka tana shafa wa kasar Sin bakin fenti ne, da zummar fakewa da haka, ta yadda za ta samu damar kara raya karfinta a fannin aikin soja.

Haka zalika, kasar Amurka tana daukar ra'ayi na kashin kai, inda take kokarin kauracewa nauyin da ya kamata ta sauke, ba tare da girmama ka'idojin kasa da kasa ba. Ya ce Gamayyar kasa da kasa sun san cewa, Amurka a kullum, na neman yin zagon kasa ga tsarin duniya, don haka ba ta da ikon yin Allah wadai da sauran kasashe a wannan fanni.

Wu ya kara da cewa, yadda Amurka take yada jita-jita game da kasar Sin ya nuna damuwarta game da tasowar kasar Sin. Sai dai jami'in ya jaddada cewa, kasar Sin za ta tsaya kan turbar raya kasa cikin lumana, da daukar manufar tsaron kasa ba tare da niyyar kai hari ga wasu ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China