Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wane abu Amurka ke tsoro matuka take yunkurin hana kasar Sin shiga zaben babban daraktan WIPO
2020-02-28 20:47:39        cri

Za a gudanar da zaben babban darektan hukumar dake sa ido, kan ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa wato WIPO a mako mai zuwa a birnin Geneva. Kasashe da dama, ciki hadda kasar Sin sun tura dan takararsu don neman wannan mukami. Amma, a gabanin wannan zabe, Amurka ta dauki wasu matakai masu ban dariya, kamar dai wani wasan kwaikwayo na siyasa.

Alal misali, sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, ya wulakanta kasar Sin, yana mai zarginta da satar ikon mallakar fasaha na sauran kasashe, har ya yi ikirarin cewa, abun dariya ne a ce za a baiwa kasar Sin ikon shugabancin WIPO, wadda take ba da taimako wajen tsara manufofin kare ikon mallakar fasaha tsakanin kasa da kasa. A sa'i daya kuma, Amurka ta matsa lamba kan wasu kasashe, don tilasta musu yin watsi da goyon bayan 'yar takarar kasar Sin, har ma ya ce, ana iya jefawa kowa kuri'u, amma ban da kasar Sin.

WIPO wata hukuma ce dake karkashin MDD, wadda take kula da aikin kare ikon mallakar fasaha na kasa da kasa. Tun kasar Sin ta shiga wannan hukuma daga ranar 3 ga watan Yuni na shekarar 1980, tana kokarin kiyaye ikon mallakar fasha, da kara hadin kanta da sauran kasashe a wannan fanni.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kara karfin kare ikon mallakar fasaha, ba ma kawai wani muhimmin mataki ne na kyautata tsarin kiyaye ikon mallakar fasaha ba, har ma yana da amfani sosai ga daga matsayin karfin takara na tattalin arzikin kasar Sin a duniya. An ce, alkaluman karfin yin kirkire-kirkire da WIPO ta gabatar a shekarar 2019 ya nuna cewa, Sin ta samu ci gaba a cikin shekaru 4 a jere, har ta kai matsayi 14 a duniya a wannan fanni.

'Yar takara da Sin ta gabatar, wato Madam Wang Binying, ita ce mataimakiyar babban daraktan WIPO na yanzu, ta kwashe shekaru 30 tana aiki a wannan hukuma, saboda haka, an ce ita ce 'yar takara mafi karfi dake da kwarewa, da hazaka matuka, da kuma fasahohi masu kyau sosai a wannan fanni.

Sin ba ta boye komai ba a cikin wannan batu, saboda ganin gudunmawar da take bayarwa, da kuma hikimar 'yar takara. A maimakon haka, Amurka ba ta gabatar da dan takararta ba, kuma ta yi biris da ka'idoji, ta kuma shafawa kasar Sin bakin fenti yadda take so. Amma matsala ita ce, shin ko wannan mataki ba fuska biyu ba ne kan wasu batutuwa, da daukar matakin babakere da kare kai ba tare da kima ba?

Amurka tana yunkurin ta da zaune tsaye a harkar zabe bisa radin kanta don kiyaye muradunta, tamkar wani wasan kwaikwayo na siyasa mai ban dariya. An yi imanin cewa, kowace kasa dake da ikon mulki ba za ta mika wuya ga Amurka ba, kuma za ta iya kada kuri'unta bisa muradunta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China