Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta hana cinye naman daji don kiyaye muhalli da bil Adama baki daya
2020-02-27 19:34:02        cri

Hukumar kafa dokokin kasar Sin wato zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta zartas da wata doka kwanan baya, wadda ta hana cinikin naman daji ba bisa doka ba a duk fadin kasar, da kuma kawar da al'ada maras kyau ta cin naman daji yadda ake so don ba da tabbacin kare lafiyar jikin jama'a. Wannan dokar da aka kafa ta ba da tabbaci ga hana yaduwar wasu kwayoyin cuta daga tushe, matakin dake da babbar ma'ana a halin yanzu da ake namijin kokarin tinkarar cutar COVID 19, kuma za ta ba da gudunmawa sosai wajen kiyaye muhalli da halittu.

Wannan doka dai ta tilasta cewa, za a hana a farauta da ciniki da kuma sufuri da cin naman daji, da kuma hana cin naman daji dake zama a kan kasa dake da babbar mana'a ga halittu, da kimiya da kuma ga al'ummar Bil Adama, da dai kuma sauran naman daji dake zama a kan doron duniyarmu, ciki hadda naman daji da bil Adama ke kokarin kiwo. Wannan doka kuma ta yi tanadi kan wane irin naman daji da ba za a iya ci ba nan gaba.

Tunanin "One Health" dake samun karbuwa sosai a duniya na nuna cewa, lafiyar jikin Bil Adama na da alaka sosai da lafiyar dabobbi da kuma muhalli. Ana fatan Bil Adama sun mutunta da kuma kula da dabobbi da kuma halittu ta yadda Bil Adama za su iya zama da sauran halittu tare cikin lumana. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China