Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha da Nijer sun fitar da shirin ba da tallafin jin kai ga marasa galihu
2020-02-27 10:17:17        cri

Gwamnatocin kasashen Habasha da jamhuriyar Nijer tare da tallafin MDD, sun fitar da shirin jin kan bil adama na shekarar 2020, kakakin MDDr ya bayyan hakan.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, game da shirin jin kan bil adama na wannan shekarar da kuma shirin ba da tallafi na jamhuriyar Nijer, MDD tana bukatar kudi kimanin dala miliyan 400 yayin da gwamnatin Nijer ke neman dala miliyan 320. Shirye shiryen guda biyu ana fatan za su taimakawa mutane marasa galihu kimanin miliyan biyu.

Ya ce jamhuriyar Nijer tana ci gaba da fuskantar matsalar kaurar jama'a sakamakon karuwar hare haren 'yan bindiga a yankunan Tillaberi da Tahoua dake yammaci da yankin jihar Diffa a kudu maso gabas, yayin da ake fama da matsalar karancin abinci gami da rashin abinci mai gina jiki dake barazana ga miliyoyin mutane a fadin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China