Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Tashin hankali na tsananta a kan iyakokin Mali, Burkina Faso da Nijar
2020-02-27 10:12:04        cri
Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (OCHA) ya yi gargadin cewa, kan iyakokin kasashen Mali da Burkina-Faso da Jamhuriyar Nijar, na fuskantar karuwar tashin hankali daga kungiyoyin masu dauke da makamai.

Stephane Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ruwaito ofishin na OCHA na cewa, 'yan tawaye masu dauke da makamai, na kaiwa makarantu hare-hare da tilastawa cibiyoyin lafiya rufewa, da ma hana al'ummomi samun kulawar muhimman hidimomi.

Ya kara da cewa, yanzu haka sama da makarantu 3,600 da cibiyoyin lafiya 241 ba sa aiki a wadannan kasashe. Yana mai cewa, a kokarin da ake na taimakawa hukumomin tarayya da na kananan hukumomi, MDD da abokan huldar ta, na tsara wasu ayyuka don ceton rayuka da kawar da kuncin da jama'a ke fuskanta, suna kuma neman taimakon kudi dala biliyan 1 don taimakawa galibin masu rauni.

Ya ce, a wannan watan kadai, an ware dala miliyan 17 daga asusun kota-kwana na MDD don baiwa kasashen Burkina-Faso da Mali, inda za su yi amfami da wadannan kudaden wajen samar da matsuguni, da ruwan sha, da tsaftar muhalli da kariya da kayayyakin kiwon lafiya da tsaron abinci. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China