Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na matukar rashin jin dadi kan zargin da Mike Pompeo ya yiwa kasar Sin
2020-02-26 20:54:28        cri

Ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya sake zargin kasar Sin ba tare da wani dalili ba, inda a jiya Talata, ya baza jita-jitar cewa wai gwamnatin kasar Sin ta kori 'yan jaridar "The Wall Street Jounal (WSJ)", matakin da ya fayyace cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta gabatar da hakikkanin bayanai dangane da cutar COVID 19 ba.

Game da wannan zargi, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, Sin ta yi matukar rashin jin dadi, tare da kalubalantar Pompeo, da kada ya rika yunkurin kunna wutar rikici tsakanin al'ummomin kasar Sin da jam'iyyar JKS da gwamnatin kasar.

An ba da labarin cewa, Zhao Lijian ya mai da martanin ne a gun taron manema labarai, yana mai cewa gwamnatin kasar Sin na gabatar da labarai game da cutar a bayyane ba tare da boye-boye ba, don sauke nauyin dake bisa wuyanta. Jaridar ta fitar da bayani, da kanun labarai mai tattare da wulakanta kasar Sin, kuma babu wata manufa ta gabatar da labarai cikin 'yanci ko kadan. Jami'in ya ce kamata ya yi daukacin al'umma su nuna adawa da wannan mataki, na nuna ra'ayin wariya da bambancin kabila. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China