Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Barkewar cutar Lassa ta yi sanadin mutuwar mutane 103 a Nijeriya
2020-02-26 13:55:58        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya NCDC, ta ce adadin wadanda suka mutu biyo bayan barkewar cutar Lassa na baya-bayan nan a kasar, ya karu zuwa 103, wanda ya kai kaso 17.6 cikin dari.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce adadin wadanda suka mutu a wannan karon, bai kai wanda aka samu a makamancin lokacin a bara ba, wanda ya tsaya kan kaso 21.1.

Tun bayan barkewar cutar a watan Junairu, ta shafi akalla jihohin kasar 26, ciki har da Jihar Lagos, cibiyar harkokin kasuwanci ta kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China