Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da kashe mayakan BH yayin wani luguden wuta ta sama
2020-02-26 13:54:52        cri
Rundunar sojin Nijeriya, ta tabbatar kashe mayakan BH da ba a san adadinsu ba, yayin wani luguden wuta ta sama a dajin Sambisa, dake zaman sansanin kungiyar.

Kakakin rundunar sojin saman kasar, Ibikunle Daramola, ya bayyana a jiya cewa, yawancin wadanda aka kashe, su ne suka kai hari na baya-bayan nan a garin Garkida na jihar Adamawa dake arewa maso gabashin kasar.

Ya kara da cewa, an kai hare-haren ta sama ne tsakanin ranekun Lahadi da Litinin, inda aka lalata gidaje da kayayyakin kungiyar dake yankin dajin Sambisa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China