Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Nijeirya ya gana da wakilan iyalai na daliban Nijeriya dake karatu a Sin
2020-02-26 11:54:27        cri

Jiya Talata, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijeriya ya kira taron ganawa da wakilan iyayen daliban Nijeriya dake karatu a kasar Sin. A yayin taron jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian, da mukaddashin shugaban sashen yankin Asiya da Pasifik na ma'aikatar harkokin wajen kasar Nijeriya, da shugaban hukumar kula da harkokin kiwon lafiya a ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Nijeirya, da shugaban kungiyar daliban Nijeriya a kasar Sin sun yi shawarwari da wakilan iyalan daliban Nijeirya dake karatu a kasar Sin sama da 30.

A yayin ganawar tasu, Zhou Pingjian ya yi bayani kan sabbin nasarorin da kasar Sin ta samu wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19 bisa matakan da kasar ta dauka, haka kuma, ya ce, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai wajen kiyaye lafiyar al'ummomin ketare dake kasar Sin, musamman ma dalibai na kasashen waje. Ya ce, kasar Sin tana kula da su kamar yadda ta ke kula da 'yan kasarta. Haka kuma, kasar Sin tana dukufa wajen warware matsalolin da 'yan kasashen ketare suke fuskanta ta hanyoyin yin musayar ra'yoyi, samar musu kayayyakin yau da kullum da kuma ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar da dai sauransu.

Wani jami'in kasar Nijeirya ya ce, kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari ya ce, a yayin da kasar Sin take fama da babbar matsala a wannan lokaci, gwamnati da al'ummomin kasar Nijeirya suna tare da ita, kuma a shirye suke su ba da taimako da goyon baya ga kasar Sin. A sa'i daya kuma, ofishin jakadancin kasar Nijeriya ya yi la'akari da daliban kasar dake birnin Wuhan da sauran sassan kasar Sin, ya kuma tabbatar da cewa, ba wanda ya kamu da cutar.

A nasu bangare, iyalai na daliban Nijeriya da suka halarci taron, sun nuna godiyarsu ga gwamnatin kasar Sin da makarantun da abin ya shafa game da taimakon da suka baiwa daliban kasar Nijeriya, sun ce, matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19 sun burge su sosai, suna kuma fatan kasar Sin za ta yi nasarar yaki da cutar da sauri, za kuma su taimakawa yaransu dake kasar Sin a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China