Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Nijeriya: Sin da Afirka suna tare da juna
2020-02-26 11:38:24        cri

Wani shehun malami a tsangayar nazarin kimiyyar siyasa ta jami'ar Abuja ta kasar Nijeirya, Sherif Ghali Ibrahim, ya fidda wani sharhi mai taken "Daga yaki da cutar Ebola zuwa yaki da cutar numfashi ta COVID-19, yadda za a habaka hadin gwiwar Sin da Afirka" a jaridar Blue Chart, a ranar 24 ga wata, inda ya yabawa kasar Sin matuka dangane da managartan matakan da ta dauka wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, ya kuma yaba matuka ga ma'aikatan lafiya dake aikin ceton wadanda suka kamu da cutar, sa'an nan, ya yi kira ga kasashen Afirka su goyawa kasar Sin baya, domin ba da gudummawarsu wajen cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Ya ce a lokacin da kasasahen Afirka suke fama da barkewar cutar Ebola, kasar Sin ta taimaka musu nan take, kuma karo na farko kasar Sin ta kafa cibiyar jinya ga wadanda suka kamu da cuttutuka masu yaduwa a kasashen ketare, yayin da ta tura ma'aikatan lafiya na fannin cututtuka masu yaduwa zuwa cibiyar, lamarin da ya nuna zumunci mai karfi dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da dangantakar 'yan uwantaka dake tsakaninsu.

Cikin sharhin, ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, kasar Sin tana fuskantar babban kalubale na barkewar cutar numfashi ta COVID-19, kuma gamayyar kasa da kasa na taimakawa kasar Sin da ba ta goyon baya, don haka ya kamata kasashen Afirka ma su goyi bayan 'yar uwansu kasar Sin, da kuma hada gwiwa da ita wajen cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China