Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta amince da dokar dakile haramtacciyar cinikayya da safarar namun daji
2020-02-24 21:39:30        cri

Zaunannen kwamitin koli na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin, wato majalisar kafa dokokin kasar ya amince da dokar dakile haramtacciyar cinikayya, da safarar namun daji a zaman da kwamitin ya yi na yau Litinin.

Karkashin dokar, an tanadi hukunta masu cinikayyar dabbobin daji, da masu sarrafa sassan jikinsu domin yin amfani da su ta hanyoyi daban daban, a wani mataki na kare lafiyar al'ummar kasa.

Kaza lika dokar za ta baiwa muhallin halittu, da na tsirrai karin tsaro, ta yadda hakan zai zamo kandagarki ga hadurran lafiya dake tattare da ta'ammali da amfani da namun daji tsakanin al'umma. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China