Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar zaben kasar Togo ta ayyana shugaba mai ci Faure Gnassingbe ne ya lashe zaben
2020-02-24 12:12:17        cri
Bisa ga cikakken sakamakon da hukumar zaben kasar Togo INEC ta fitar ya nuna cewa, shugaban kasar mai ci Faure Gnassingbe ya lashe zaben wanda aka kammala a ranar Asabar bayan da ya samu kashi 72.36 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada.

Gnassingbe ya yiwa abokan takararsa gagarumar tazara, daga cikinsu akwai tsohon firaministan kasar kana tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Messan Agbeyome Kodjo, wanda ya samu kashi 18.37 bisa 100, sai tsohon jagoran 'yan adawar kasar Jean-Pierre Fabre, wanda ya samu kashi 4.35%, a cewar hukumar ta INEC.

Bisa ga sakamakon da aka samu, Tchambakou Ayassor, shugaban hukumar zaben kasar INEC, ya ayyana Gnassingbe, dan takarar Jam'iyyar Union for the Republic, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Togo.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China