Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin ketare dake kasar Sin sun dawo bakin aiki
2020-02-21 20:45:52        cri
Jiya Alhamis 20 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaran aikinsa na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in bisa gayyatar da aka yi masa, inda ya yi nuni da cewa, annobar cutar numfashi ta COVID-19 ba za ta kawo tasiri ga hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da musanyar tsakanin al'ummomin kasashen biyu na dogon lokaci ba, tasirin na kankanin lokaci ne kawai, yanzu ba ma kawai kamfanonin Koriya ta Kudu ba, wasu kamfanonin ketare ma sun dawo bakin aiki daya bayan daya, bisa sharadin dakile yaduwar cutar.

Kawo yanzu adadin manyan kamfanonin ketare dake birnin Shanghai da lardin Shandong da lardin Hunan da sauran sassan kasar ta Sin wadanda suka dawo bakin aiki ya kai kaso 80 bisa dari, an yi hasashen cewa, yawancin kamfanonin ketare dake kasar Sin za su dawo bakin aiki nan da karshen wannan watan da ake ciki, duk wadannan sun nuna cewa, kasuwar kasar Sin wadda ke da adadin al'ummun biliyan 1 da miliyan 400 tana jawo hankulansu matuka, saboda kamfanonin ketare dake kasar Sin suna ganin cewa, tasirin da annobar take haifar wa tattalin arzikin kasar zai ragu cikin kankanin lokaci, tattalin arzikin kasar zai ci gaba da samun bunkasuwa mai dorewa, a don haka bai dace ba a rika baza jita-jitar cewa, kamfanonin ketare za su dakatar da aikinsu a kasar Sin, har za su bar kasar.

A kokarin da ake yi na taimakawa kamfanonin ketare wajen ganin sun dawo bakin aiki, gwamnatin kasar Sin ta dauki makatai a jere, inda ta bayyana cewa, ba za a nuna bambanci ga kamfanonin kasar Sin da kuma kamfanonin ketare ba, haka kuma za ta taimaka domin sun ci gajiya daga manufofinta na dakile annobar. A sa'i daya kuma, kamfanonin ketare dake kasar Sin su ma sun samar da tallafi ga kasar Sin yayin da take kokarin ganin bayan annobar. Alkaluman sun nuna cewa, ya zuwa ranar 14 ga wata, gaba daya adadin tallafin kudi da kayayyakin da kamfanonin ketare suka samar ya kai dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 760.

Annobar COVID-19 ba za ta rage bukatun kasuwar al'ummun kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 400 ba, haka kuma ba za ta kawo tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar mai dorewa ba, kana kasar Sin ba za ta sauya aniyyarta ta kara yin kwaskwarima a gida da kuma bude kofa ga ketare ba, ko shakka babu kamfanonin ketare dake nan kasar Sin wadanda ke hada kai da kasar Sin domin dakile annobar za su samu ci gaba tare da kasar Sin yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China