2020-02-21 13:21:01 cri |
Cikin wata sanarwa, kakakin shugaban al'ummar falasdinawa Nabil Abu Rudeineh, ya ce "Netanyahu ya kafe sai ya gina sabbin matsugunan Yahudawa, domin lalata burin kafa kasashe biyu masu cin gashin kan su, wanda hakan mataki ne na aiwatar da kudurin Amurka, karkashin abun da Amurkar ta kira yarjejeniyar karni da ta gabatar,".
Nabil Abu Rudeineh ya kara da cewa, Netanyahu na yunkurin samun yardar Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi ne gabanin zaben dake tafe, ba tare da la'akari da bukatun al'ummmar falasdinu ba. Ya ce akwai bukatar sassan kasa da kasa su yi hanzarin shiga tsakani, don dakile wannan mataki na Isra'ila.
Kafin hakan, Mr. Netanyahu ya ayyana kudurin gwamnatin sa, na gina sabbin matsugunan Yahudawa har 5,200 a yankunan gabashin birnin Kudus da ake takaddama a kan su. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China