Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijar: Tashe-tashen hankula sun jefa mutane miliyan 3 halin kunci
2020-02-20 11:07:32        cri

Ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, ya ce kusan mutane miliyan 3 sun tsunduma cikin matsananciyar bukatar tallafi a jamhuriyar Nijar, sakamakon tashe-tashen hankula da sauran wasu dalilai daban daban.

Ofishin na OCHA ya ce, sama da rabin wannan adadi dai kananan yara ne da suka shiga wahalhalu, saboda matsalolin tsaro dake shafar kasashe makwaftan kasar, wanda hakan ya haifar da kwararar masu neman mafaka, da masu komawa kasar daga wasu sassa, da masu kaura a cikin kasar da 'yan ci rani.

Ofishin ya ce dukkanin wadannan rukunoni na mutane na bukatar muhimman abubuwan bukata na rayuwa, da hidimomin raya zamantakewa, da kuma kariya ga rayukansu.

A daya bangaren kuma, asusun yara na MDD UNICEF, ya ce ma'aikatan sa dake aiki a yankin, suna jan hankalin masu ruwa da tsaki da su tallafawa yara kanana da iyalansu. Kaza lika UNICEF ya jinjinawa mahukuntan jamhuriyar Nijar, bisa karamcin da suka nunawa wadanda ke cikin mawuyacin hali.

Rahotanni daga asusun na yara sun cewa, wasu hare-hare daga kasar Chadi mai makwaftaka da Nijar ta gabashi, sun hana mutane kusan 263,000 komawa gida. Bugu da kari, tabarbarewar yanayin tsaro a Burkina Faso da kasar Mali ta bangaren yammaci na kara ta'azzara, wanda hakan ya raba mutane da yawan su ya kai 78,000 da muhallan su.

A bangaren Najeriya mai makwaftaka da Nijar ta kudanci kuwa, mutane sama da 35,000 ne suka tsere zuwa sassan kauyukan Nijar ta kan iyakar kasashen biyu.

Har ila yau, akwai kimanin mutane 260,000 a Nijar din, wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, yayin da yara kanana 380,000 ke fuskantar barazanar karancin abinci mai gina jiki, kana wasu yaran 600,000 ke fuskantar yiwuwar tsunduma cikin wasu nau'o'in annoba. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China