Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen duniya sun nuna adalci wajen jinjina yadda Sin ke fama da cutar COVID-19
2020-02-19 22:01:00        cri
A ranar 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron da kuma firaministan kasar Birtaniya Boris Johnson bisa gayyatar da suka yi masa. A wannan muhimmin lokacin da Sin ke yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kasashen duniya na kara gaisuwa da karfafa gwiwa ga kasar Sin, tare da jinjina kokarin Sin na fama da cutar cikin adalci, baya ga nuna aniyarsu ta yin hadin gwiwa da goyon bayan Sin a fannin shawo kan cutar.

Ana iya lura da cewa, yayin da Xi ya yi magana da su, ya nuna ra'ayoyinsa a fannoni uku, wato na farko yanayin dakile yaduwar cutar ya yi sauki, matakan rigakafin ma sun haifar da sakamako mai kyau. Na biyu, Sin na da imani da ma kwarewa wajen cimma burin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta a bana. Na uku kuma shi ne, Sin za ta ci gaba da hada kai tare da kasashen duniya ba tare da boye komai ba.

Duk wadannan ra'ayoyin uku sun kasance martani mai yakini da Sin ta mayar wa kasashen duniya kan goyon bayan da suka nuna mata.

A halin yanzu, sakamakon ci gaban da aka samu a bayyane wajen shawo kan cutar, ya sa an fara aiki a wurare daban daban na kasar Sin. Shin Sin za ta iya cimma burin da ta sanya a gaba a bana ko a'a? Wannan ya kasance wani abun da duniya ta fi mayar da hankali a kai. "Muna da imani da kwarewa", wannan shi ne amsar da shugaban kasar Sin ya bayar. Ya fadi haka ne, saboda karfin halin da ya ke da shi kan karfin tattalin arzikin Sin, da yawan bukatun cikin gida, da ma tushen masana'antu mai inganci.

Babu shakka wannan annoba ta shafi daukacin bil Adam, kuma kasar Sin ta sa duniya ta fahimta cewa, hadin gwiwa da imani sun fi komai daraja. A wannan zamanin da duniya ke kokarin dunkulewa gu daya, babu wata kasa da za ta iya tinkarar wata matsala ita kadai. Jama'ar Sin ba za su manta da goyon baya da taimakon da kasashen duniya ke ba ta ba. Annobar za ta wuce. Hadin gwiwar da aka samu a lokacin da aka fuskanci matsala za ta kara samar da sabuwar dama ta inganta hadin kai a tsakaninsu a nan gaba.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China