Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin samar da kayayyaki na Sin sun sake fara aiki
2020-02-18 21:36:33        cri

A farkon watan Febrairu na bana, Sin ta dakatar da aikin samar da kayayyaki a sakamakon bullar cutar numfashi ta COVID-19, sai dai kamfanin kera motoci na Hyundai na kasar Koriya ta Kudu ya dakatar da kera motocinsa.

A ranar 17 ga wannan wata, bayan da wasu kamfanonin kasar Sin suka fara aikin samar da kayayyaki bisa goyon bayan gwamnatocin kasashen Sin da Koriya ta Kudu, kamfanin Hyundai ya tsaida kudurin dawo da yawancin aikin kera motocinsa.

Wadannan labarai biyu da aka bayar a cikin kwanakin fiye da 10 sun shaida cewa, Sin ta kasance mai muhimmanci a fannin samar da kayayyaki a duniya. A yayin da ake samun nasarori a matakan kandagarki da hana yaduwar cutar a kasar Sin, kamfanoni da dama na Sin sun dawo da ayyukansu da ci gaba da samar da kayyayaki, ba domin moriyar kansu kawai ba, hatta ma sun kiyaye samar da kayayyaki a duniya da tabbatar da moriyar dukkan duniya baki daya.

A ranar 10 ga wannan wata, kamfanonin Sin sun sake fara aiki sannu a hankali bisa yanayin magance da yaki da cutar yadda ya kamata. A halin yanzu, ban da lardin Hubei, kamfanonin larduna da birane da yankuna 30 na babban yankin kasar Sin sun fara aiki. An gano cewa, gwamnatin tsakiya ta Sin da gwamnatocin wurare daban daban na Sin sun rage kudin da ake kashewa kan tattara kudi, da ba da rangwamen haraji, da tabbatar da ayyukan jama'a da sauransu don samar da yanayi mai kyau na farfado da ayyukan kamfanoni. Yayin da kamfanoni ke dawowa bakin aiki, ya kamata a gudanar da bincike da duba yanayin lafiyar kowane ma'aikacin kamfanonin. Wannan ya hada da aikin magance da yaki da cutar da farfado da ayyukan kamfanoni.

Kamar yadda forfesa Robert C. Merton na kwalejin MIT wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel a fannin tattalin arziki ya bayyana a cikin wasikarsa da ya rubuta wa jama'ar kasar Sin cewa, akwai kyakkyawar fatan samun bunkasuwar tattalin arzikin Sin a dogon lokaci, kana ya yi imani da cewa, kasar Sin za ta kara samun karfi bayan da ta cimma nasarar yaki da cutar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China