Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala taron tsaro na Munich ba tare da cimma matsaya game matsayin kasashen yamma ba
2020-02-17 12:01:04        cri

An kammala taron tsaro na Munich wato MCS karo na 56 a jiya Lahadi, inda mahalarta taron suka kasa cimma matsaya dangane da matsayin kasashen yamma wato "Westlessness" dake zaman taken taron na bana.

Akwai yiwuwar muhawarar da aka yi kan taken taron wanda ke nufin matsayin kasashen yammacin duniya na raguwa, zai ci gaba da gudana.

A jawabinsa na rufe taron, shugaban MSC Wolfgang Ischinger, ya ce akwai bambancin ra'ayi tsakanin abokan hulda na kasashen Tarayyar Turai da na Amurka, yana mai jaddada cewa, idan har ba a saurari ra'ayoyin juna ba, to lallai za a samu matsaloli.

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi kira da a kawar da banbancin dake akwai tsakanin bangaren gabashi da yammacin duniya tare da inganta hulda tsakanin kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China