Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka mutu a harin kauyen dake tsakiyar Mali ya kai 31
2020-02-16 15:33:42        cri

Firaministan kasar Mali Boubou Cisse ya ba da tabbacin karuwar yawan mutanen da suka mutu a harin da aka kaddamar ranar Juma'a kan kauyen Fulani Ogossagou dake tsakiyar kasar, adadin ya kai 31.

A sakon ta'aziyyar da ya aikewa iyalan wadanda harin ya rutsa da su ta shafinsa na sada zumunta, Cisse ya ce, a yayin da suke ci gaba da kokarin tura dakarun tsaro zuwa sassan kasar domin wanzar da zaman lafiya, kauyen Ogossagou ya fuskanta wani sabon kazamin hari wanda aka hallaka mutane 31.

Sai dai kuma, wasu majiyoyi masu zaman kansu sun ce, adadin mutanen da suka mutu ya kai 48, kuma daga cikin gawarwakin da aka gano har da wasu mata masu juna biyu su biyar.

Masu nazarin al'amurra da dama sun yi amanna cewa harin, wanda mayaka kusan 30 suka kaddamar, ya faru ne sakamakon janye dakarun tsaron kasar Mali daga yankin da lamarin ya faru.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China