Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattaunawar da jakadan kasar Sin a Amurka ya yi tare da dan jaridar kasar
2020-02-15 19:53:13        cri
A ranar 13 ga wata, jakadan kasar Sin a Amurka Cui Tiankai, ya tattauna da Steve Inskeep, mai gabatar da shirin Morning Edition na gidan rediyon NPR na Amurka, inda ya amsa tambayoyin da aka masa dangane da cutar numfashi da kwayar cutar corona ke haddasawa.

A game da tambayar ko barkewar cutar ta zama babbar barazana ga kasar Sin, jakadan ya ce, wannan babban kalubale ne ga kasar Sin, haka ma ga duniya baki daya. Ya ce yayin da ake samun ci gaban zaman al'umma da tattalin arziki, yadda za a daidaita matsalar lafiyar al'umma da kuma tinkarar cuta irin wannan, kalubale ne ga kasashen duniya baki daya da kuma gwamnatocinsu. Wasu na cewa, wannan kalubale ne da ba a taba ganin irinsa ba, kuma matakan da aka dauka ma sun kasance wadanda ba a taba gani ba. Jakadan ya ce wannan gaskiya ne, kasar Sin na iyakacin kokarin shawo kan cutar, da kuma saukaka illolin da cutar ke haifarwa ga tattalin arziki da zaman al'umma.

A game da batun canza wasu manyan jami'an lardin Hubei da cutar ta fi kamari a kwanan baya, jakadan ya ce, dukkanin matakan da aka dauka, ciki har da canza jami'an, na da buri daya, wato amsa kirar jama'a da kuma biyan bukatunsu. Yana mai cewa wannan ya kasance buri daya tilo na kasar Sin wajen daukar dukkanin matakai. A irin wannan hali na musamman, babu shakka za a kara dora nauyi ga wadanda ke da kwarewa.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China