Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron MSC
2020-02-15 16:49:39        cri

An bude taron Munich kan harkokin tsaro karo na 56 a birnin Munich da ke kudancin kasar Jamus a jiya Jumma'a, inda mahalarta taron suka tattauna batun dakushewar kasashen yammacin duniya da ma sauran batutuwan kasa da kasa da ke jan hankalin duniya.

A jawabinsa na bude taron, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana cewa, manufar nan ta "mu kasashen yammaci" ba ta samun karbuwa sosai kamar yadda ta yi a da, ko a fannin zaman al'umma ko kuma a fannin manufofin diplomasiyya da na tsaro, kuma taron na wannan karo zai mai da hankali kan batun.

Shugaban taron Wolfgang Ischinger ya ce, a halin da kasashen duniya ke fuskantar babbar barazana ta fannonin zaman lafiya da tsaro, kasa da kasa ba su kai ga daukar matakai na bai daya ba. Ya ce mu'amala da juna shi ne mataki na farko na daidaita matsaloli da rikici, don haka yake fatan taron zai samar da dandali na mu'amala tsakanin sassa daban daban.

Bisa ajandar taron, za a kuma tattauna arangamar da ke tsakanin Jamus da Amurka kan bututun man gas da halin da ake ciki a gabas ta tsakiya, sai kuma tsaron yanayi da tsaron sararin samaniya da tsattsauran ra'ayi da kalubalen da fasahohi da kirkire-kirkire ka iya haifarwa ta fannin tsaro.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China