Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wen Shangbang da uwargidansa
2020-02-12 15:45:58        cri

 

 

 

 

 

Wen Shangbang ke nan tare da uwar gidansa Zhao Qing, wadanda dukkansu likitoci ne a kauyen Huangxi da ke gundumar Datong mai zaman kanta, ta kabilar Hui da ta Tu ta lardin Qinghai na kasar Sin. Domin dakile yaduwar cutar coronavirus, ma'auratan suna shan aiki. Kowace rana da safe da misalin karfe 8, su kan fara aiki. Mr. Wen Shangbang ya kan tafi da akwatin magunguna, ya je gidajen mazauna kauyen, don auna zafin jikinsu, a yayin da uwar gidansa take zama a asibiti, tana samar da jiyya ga wadanda ba su da lafiya. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China