2020-02-09 20:32:06 cri |
Tun bayan barkewar cutar, gwamnatin Sin ba ta bata lokaci ba, inda nan take ta gudanar da bincike, da gano ainihin nau'in kwayar cutar, gami da bayyanawa WHO, da sauran kasashe yadda wannan kwayar cutar take. Baya ga haka, ta dauki kwararan matakai na dakile yaduwar cutar, matakan da suka samu amincewa da goyon baya daga kasa da kasa. Duk da haka, wasu 'yan siyasa da kafofin yada labarai na kasashen yammaci suka yi ta samar da labaran da ba na gaskiya ba, don shafawa kasar Sin bakin fenti, matakan da suka keta hakkin Sinawa mazauna ketare, wadanda kuma suka kawo cikas ga hadin gwiwar kasa da kasa ta fannin shawo kan cutar.
Kwayoyin cuta abokan gaba ne ga 'yan Adam baki daya. Yadda kasar Sin ke daukar kwararan matakai na dakile yaduwar cutar, ba ma kawai don kare al'ummarta ba ne, har ma don kare al'ummar duniya baki daya.(Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China