Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin zaman lafiyar Amurka yana kunshe da take dokokin kasa da kasa 300, in ji jami'in Falastinawa
2020-02-09 16:55:26        cri
Wani babban jami'in al'ummar Falastinawa ya bayyana cewa shirin zaman lafiyar Amurka, wanda aka fi sani da "yarjejeniyar karni", yana kunshe da saba dokokin kasa da kasa kimanin 300.

Ahmad Majdalani, mamba kungiyar fafutukar kwato 'yancin al'ummar Falastinawa ta (PLO), ya fadawa manema labarai cewa, shugaban Falastinawa Mahmoud Abbas zai gabatar da batutuwan da suka shafi saba dokokin kimanin 300 a gaban kwamitin sulhun MDD a birnin New York a ranar Talatar makon gobe.

A ranar Litinin shugaban Falastinawan zai isa Amurka, kuma zai gabatar da jawabi a gaban kwamitin sulhun MDDr game da yarjejeniyar ta Amurka a ranar Talata, inda zai gabatar da kuduri don kada kuri'a kan kudurin a tsakaninn mambobin kwamitin MDD.

Majdalani yace, bayanan dake tabbatar da saba dokokin kasa da kasar kungiyar PLO ta riga ta tsara shi.

Yace yarjejeniyar da Amurkar ta tsara tana kunshe da danne hakkin Falastinawa da kuma hana al'ummar Falastinawa cikakken 'yancinsu na samun 'yantacciyar kasa.

Haka zalika Mahmoud Aloul, mataimakin shugaban jam'iyyar Fatah ta shugaba Abbas ya ce, a yayin da shugaban Mahmoud Abbas ke gabatar da jawabin a gaban kwamitin MDD, magoya bayansa zasu gudanar da zanga zanga domin nuna goyon bayansu gare shi a ranar Talatar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China