Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Falasdinu ya ce gabashin birnin Kudus ne kadai zai iya zama babban birnin Falasdinu
2020-02-07 11:06:42        cri
Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas, ya jadadda cewa, gabashin birnin Kudus ne kadai zai iya zama babban birnin Falasdinu maimakon Abu Dis.

Kamfanin dillancin labarai na Falasdinu WAFA, ya ce shugaban ya bayyana yayin wani taron da ya yi da fitattun kungiyoyi da kungiyoyin al'umma, jiya a birnin Ramalla dake matsayin hedkwatarsa cewa, ba zai amince da duk wani zabi da yarjejeniyar zaman lafiya ta Donald Trump kan yankin Gabas ta Tsakiya ta tanada ba.

Ya kara da cewa, ba za su amince da zama kasa ba tare da samun gabashin birnin kudus da aka mamaye a 1967 a matsayin babban birnin Falasdinu na har abada ba.

Mahmoud Abbas ya ce za su yi fito-na-fito da batun har sai sun ci nasara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China