Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Erdogan da Putin sun zanta game da harin dakarun Syria a Idlib
2020-02-05 11:24:21        cri
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da takwaran sa na Rasha Vladimir Putin, sun tattauna ta wayar tarho a jiya Talata, game da harin da sojojin kasar Syria suka kaddamar kan sojojin Turkiyya dake birnin Idlib a ranar Litinin.

Kafar watsa labarai ta TRT mallakar kasar Turkiyya, ta rawaito shugaba Erdogan na shaidawa Putin cewa, harin na dakarun Syria kan sojojin kasar sa, ya lahanta yunkurin hadin gwiwa na wanzar da zaman lafiya da ake yi a Syria. To sai dai kuma Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da amfani da hakkin ta na tsaron kai, ta dukkanin hanyar da ta ga ta dace komai tsaurin ta.

Tuni dai Turkiyya ta kai hari sau 54 kan wasu wurare a Syria, lamarin da ya haifar da kisan dakarun Syria 76 a yankin na Idlib, wanda shi ne tungar karshe ta 'yan tawayen kasar, a matsayin ramuwar gayyar kisan sojojin ta su 8. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China