Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres: MDD ta himmantu kan shirin zaman lafiyar Israila da Falastinu
2020-02-05 11:20:44        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce MDDr ta damu wajen ganin an warware batun takaddama tsakanin kasashen Isra'ila da Falastinu.

Jami'in MDDr ya fada a taron manema labarai game da muhimman ayyukan da MDD za ta mayar da hankali kan su a shekarar 2020 cewa, a shirye suke su tabbatar da samun maslaha game da takaddamar dake tsakanin kasashen biyu. Kuma MDD ta himmantu wajen goyon bayan dukkan hanyoyin da za su kawo dawwamamman zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falastinu da kuma dukkan matakan da za su samar da hanyar warware rikicin bangarorin biyu karkashin yarjejeniyar dokokin kasa da kasa, da kudurin kwamitin sulhun MDD da kuma yarjejeniyar babban taron MDD wanda ya amince da shata kan iyakokin kasashen biyu a shekarar 1967.

Babban sakatare ya ce, "Matsayarmu a bayyane take. Muna bin ka'idojin MDD da dokokin kasa da kasa."

"Ba za mu canza matsayarmu ba." in ji shi.

A ranar 28 ga watan Janairu, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gabatar da wani shirin zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya mai cike da rudani, wanda ya bayyana shi da cewa "Yarjejeniyar karni," inda ya bayyana shirin da cewa hanyar zaman lafiyar ne sai dai ya ayyana Jerusalem a matsayin babban birnin Isra'ila wanda ba za'a taba raba shi ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China