Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai domin kiyaye alummomin kasa da kasa
2020-02-04 20:22:19        cri

Kwanan baya, kwalejin nazarin al'amuran kasa da kasa na Shanghai ya kaddamar da wani rahoto, inda ya tantance ci gaban da kasar Sin ta samu a kwanakin baya wajen shawo kan annobar cutar numfashi, illar da watakila za ta biyo baya da kuma matakan da za ta dauka.

Dangane da dalilin da ya sa kasar Sin ta dauki wasu matakai masu karfi, kamar hana kaiwa da komowar mutane daga birnin Wuhan, rahoton ya bayana cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne domin hana yaduwar annobar zuwa sauran sassan kasar, wannan mataki ne da ba a taba dauka a baya ba domin daidaita matsalar da ta shafi lafiyar al'umma, kuma mataki ne da kasar Sin ta dauka domin sauke nauyin dake bisa wuyanta. Wadannan matakai sun ba da kariya ga al'ummar kasar ta Sin da ma al'ummomin kasa da kasa baki daya.

Rahoton ya yi nuni da cewa, bayan barkewar annobar, kasar Sin ta kafa wani cikakken tsari mai kunshe da gwamnati, kamfanoni da zaman al'ummar kasa da kasa domin yaki da annobar tare, ta kuma karfafa gwiwar al'ummar kasar ta Sin wajen yaki da annobar.

Rahoton ya yi bayani da cewa, mai yiwuwa ne barkewar annobar za ta kawo illa kai tsaye kan wasu sana'o'in ba da hidima, samar da kayayyaki, da ciniki. Amma kada a manta da karfin kasar Sin na raya tattalin arziki. A cikin gajeren lokaci, barkewar annobar tana amfanawa bunkasuwar harkokin kasuwanci kan Intanet, wasanni kan Intanet wato Netgames a Turance da kuma kamfanonin nishadi. A cikin dogon lokaci mai zuwa ma, a matsayinta na rukuni na 2 a duniya ta fuskar ci gaban tattalin arziki, boyayyen karfin da kasar Sin take da shi ba zai bace ba sakamakon barkewar annobar.

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, yayin da kasar Sin take yaki da annobar, ba ta manta da nauyin da aka dora mata ba. Ta sanar da barkewar annobar ba tare da rufa-rufa ba. Ta kuma yi iyakacin kokarin hana yaduwar annobar zuwa sauran sassan duniya ta hanyoyi daban daban.

Sakamakon dinkuwar duniya baki daya ya sa, barkewar annobar za ta kawo illa ga duk duniya. Rahoton ya ba da shawarar cewa, kamata ya yi kasashen duniya su kara kyautata tsarin sanar da barkewar annoba. Ya kuma jaddada cewa, dole ne a magance yaduwar annobar ta dakatar da yin mu'amala tsakanin kasa da kasa, a maimakon haka, za ta kyautata hadin gwiwar da ke tsakanin al'ummomin kasa da kasa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China