Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kila Birtaniya za ta tinkari karin wahalhalu tun bayan ficewarta daga EU
2020-02-01 20:09:16        cri
Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai EU a hukumance da misalin karfe 11 na daren jiya Juma'a agogon GMT, bayan ta shafi shekaru uku da rabi tana kokarin bari. Ko da yake firaministan kasar Birtaniya Boris Johnson ya sanar da cewa, kasarsa za ta shiga wani sabon zamani, amma la'akari da wasu rashin tabbas da dangantakar da ke tsakanin Birtaniya da EU, da sauyin yanayin siyasa na bangarori da dama ke haddasawa, ana damuwa da makomar kasar sosai.

Wani sharhin da BBC ya watsa na ganin cewa, a matsayinta ta mambar farko da ta janye jiki daga EU a tarihi, wannan batu zai kasance sauyi mafi girma a yanayin siyasar kasashen Turai tun bayan yakin cacar baki. A idon shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, batun ficewar Birtaniya daga EU ya kawo wa kasarta da EU babbar barna. Dimbin mutane na damuwa da cewa, mai yiwuwa wata mambar kungiyar ta dauki matakin ficewa nan ba da dadewa ba. Don haka yadda za a gaggauta matakan kawar da sabannin da ke cikin kungiyar, da sa kaimi ga yunkurin dunkulewar Turai gu daya na da matukar muhimmanci.

Ficewar Birtaniya za ta kara azama ga EU wajen daidaita tsarin muradun bangarori daban daban. Babu shakka yawan kudin da za a kashe wajen cinikayya a tsakanin Birtaniya da kungiyar zai karu. Ban da wannan kuma sakamakon raunanar matsayin birnin London a fannin hada-hadar kudi, biranen Paris da Frankfurt za su samu damar karfafa tasirinsu ta fuskar tattalin arziki. Amma bayan ficewar Birtaniya, EU za ta fuskanci matsalar gibin kudade EURO biliyan 10 a kowace shekara. Lamarin da ya sa kasashe mambobi 27 na kungiyar yanzu ke bukatar nazari sosai kan yadda za su habaka hanyoyin samun kudin shiga da ma rage yawan kudin kashewa.

A bangaren Birtaniya kuma, batun ficewar ya illata zamantakewar al'ummar kasar. Domin ya sha suka sosai daga wasu 'yan kasar, inda har yankin Scotland ke yunkurin janye kansa daga kasar. Game da dangantakar da ke tsakanin Birtaniya da ketare, yadda Birtaniya da EU ke ciyar da dangantakarsu gaba zai zama wani muhimmin batu. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, dole ne Birtaniya ta samu sabon matsayin da ya dace da sabon yanayin da take ciki.

Shin Birtaniya da ta samu 'yanci daga hannun EU za ta samu sabuwar makoma? Wane irin tasiri ficewar kasar daga EU zai yi a duniya a nan gaba? Watakila, sai zuriyoyin gaba ne za su samu amsa. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China