Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakile yaduwar cutar numfashi ya bayyana yadda gwamnatin kasar Sin ke kare hakkin dan Adam
2020-01-28 17:07:55        cri

Yayin da ciwon numfashin da kwayar cuta ta coronavirus ke haddasawa ke ci gaba da yaduwa a kasar Sin, al'ummar kasar na zama tsintsiya madaurinki daya domin yaki da wannan annoba. Kuma irin managartan matakan dakile yaduwar cutar da gwamnatin kasar ke dauka ba tare da bata lokaci ba, kuma ba tare da wata rufa-rufa ba, sun samu amincewa da goyon-baya daga kasashe da dama.

Amma duk da haka, akwai wasu kafofin watsa labaran kasashen yammacin duniya, wadanda suka bayyana cewa, kasar Sin ta kambama yanayin da ake ciki ta hanyar daukar matakan da suka wuce gona da iri, har ta kai ga keta hakkokin dan Adam. Gaskiya wannan zargin da aka yiwa kasar Sin ba gaskiya ba ne, kuma ba bu tausayi cikin sa ko kadan, kawai wasu kasashen yammacin duniya na son shafawa kasar Sin kashin kaji bisa hujjar kare hakkin dan Adam ne.

Wannan sabon nau'in ciwon numfashin da kwayar cutar nan ta coronavirus ke haddasawa, na iya bazuwa tsakanin bil adama cikin sauki, ga shi kuma an samu barkewarsa a daidai lokacin da al'ummar kasar Sin ke yawaita tafiye tafiye a sakamakon shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyarsu, abun da ya sa annobar ke kara yaduwa, da haifar da babbar barazana ga lafiyar dan Adam.

Zuwa jiya Litinin, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 4515 a wasu jihohi da birane 30 na kasar, har ma ana samun wadanda suka kamu da cutar a sauran wasu kasashe. A cewar masana harkokin kiwon lafiya, daya daga cikin muhimman matakan dakile yaduwar cutar shi ne, hana yawan zirga-zirgar al'umma, da rage mu'amala tsakanin dan Adam, ta yadda za'a katse hanyar bazuwar kwayar cutar, da kuma shawo kan annobar baki daya.

Gwamnatin kasar Sin na nuna kwazo, wajen daukar matakan kandagarkin yaduwar cutar, ciki har da killace birnin Wuhan na wani gajeren lokaci, da soke manyan bukukuwa ko gangamin jama'a, da tsawaita lokacin hutun bikin shiga sabuwar shekara na Sinawa, matakan da za su taimaka sosai ga kiyaye tsaron al'umma, da bada gudummawa ga harkokin lafiya na duk duniya, wadanda suka dace da ka'idojin kasa da kasa ta fannin dakile yaduwar annoba.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China