2020-01-25 16:21:53 cri |
Yawan al'ummar kasar Sin ya kai biliyan 1.4, masu matsakaicin kudi shiga, wadanda ke kara samun karfin yin sayayya. Har wa yau, gwamnatin kasar na kara daukar matakan saukaka shigar da kayayyaki daga kasashen waje, ta yadda kaya masu inganci na kasashe daban-daban za su samu damar shiga kasuwar kasar Sin cikin sauki. Kana kuma, sana'ar kasuwanci ta kafar sadarwar Intanet tsakanin kasa da kasa na taimakawa kasashe daban-daban fitar da kayayyakinsu zuwa kasar ta Sin.
Kasar Sin na fadada bude kofarta ga kasashen waje ta hanyar daukar wasu matakan da suka dace, al'amarin kuma da ya aza tubalin tattalin arziki mai inganci domin tinkarar kalubale da hadurra. Duk da cewa akwai barkewar wani nau'in cutar numfashi a sassa daban-daban na kasar Sin a yayin da Sinawa ke murnar shiga sabuwar shekara, babu tantama za'a iya shawo kansa kuma kasuwar kasar Sin za ta ci gaba da maraba da shigowar kayayyaki masu inganci daga kasashe daban-daban.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China