Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kusan 1/3 na yara mata daga iyalai matalauta ba su samu damar shiga makarantu ba, in ji UNICEF
2020-01-21 12:20:43        cri
Jiya Litinin, asusun tallafawa kanannan yara na MDD wato UNICEF ya fidda rahoton cewa, kimanin kashi 1 bisa 3 na yara mata 'yan tsakanin shekaru 10 zuwa 19 da suka fito daga iyalai masu fama da talauci a duniya ba su samu damar shiga makarantu ba.

Rahoton mai taken "yadda za a fuskanci kalubalen koyon ilmi: ana matukar bukatar kara zuba jari domin taimakawa yara na gidaje mafi fama da talauci kan harkokin koyon ilmi" ya nuna cewa, talauci, da nuna bambancin jinsi, nakasar jiki, rashin iya harsuna da rashin ingancin ababen more rayuwa su ne dalilan da suka haddasa rashin samun karatu, lamarin da ya sa, ba su iya samun damammaki da fasahohi na kawar da talaucinsu ba, a sa'i daya kuma, ya tsananta kalubalolin samar da ilmi da yin karatu na kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China