2020-01-20 16:03:21 cri |
A birnin Wuhan inda cutar ta fara bulla, ya zuwa ranar Asabar din karshen makon jiya, mutane 3 sun rasu sakamakon kamuwa da cutar. Kaza lika yawan sabbin wadanda suka kamu da ita ya kai mutum 136, tsakanin ranekun Asabar da Lahadin karshen mako, kamar dai yadda hukumar lafiya ta yankin ta sanar. Hukumar ta ce kafin ranar Asabar din, masu dauke da cutar na fama da zazzabi, da tari, da shakewar kirgi.
An dai samu mutane 2 dake dauke da wannan cuta mai nasaba da sanyin hakarkari ko "pneumonia" a birnin Beijing, da kuma mutum guda a birnin Shenzhen, a karon farko tun bayan da cutar ta bayyana a Wuhan. An kuma ce a baya bayan nan, dukkanin mutanen 3 sun yi balaguro zuwa birnin na Wuhan. (Saminu Hassan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China