Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Beijing: Tallafawa matalauta ta hanyar sayen kayayyakin da suka samar
2020-01-20 12:27:25        cri

 

Sauran kwanaki 4 a yi bikin bazara a kasar Sin, wato bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar. Yanzu haka jama'a na kokarin sayen kaya a wata kasuwar dake unguwar Cao Qiao ta birnin Beijing, don samun kayayyakin da ake bukata a lokacin biki, gami da tallafawa matalauta, wadanda suka samar da kayayyakin. Wannan kasuwa, an kafa ta ne musamman ma domin taimakawa matalauta sayar da kayayyakin da suka samar. Yanzu haka ana samun cunkuson jama'a a cikin kasuwar, wadanda suke sayen dabinon da aka samar da shi a jihar Xinjiang, da naman shanun lardin Qinghai, gami da shinkafar da aka samar da ita a jihar Mongoliya ta gida, da dai sauran abubuwan da ake bukata yayin bikin bazara dake tafe. An ce dukkan nau'ika fiye da 1500 na kayayyakin da ake sayar da su cikin kasuwar, an samar da su ne a wasu yankuna masu fama da talauci.

Wani dattijo mai suna Wang ya zo wajen kasuwar a karon farko, amma ya sayi abubuwa da yawa tare da nuna gamsuwa, a cewarsa,

" Kayayyakin da ake sayar ba su da tsada. Na sayi abincin jihar Xinjiang, da naman shanu, gami da shinkafa. Manufar kasuwar tana da kyau. Saboda ta ba jama'a damar sayen kayayyaki masu sauki, gami da taimakawa talakawa samun ci gaban harkokinsu."

Sauran masu sayen kaya su ma sun gaya mana cewa, dalilin da ya sa suka zo wannan kasuwar, shi ne domin kayayyakin da ake sayar a nan suna da inganci, gami da araha, sa'an nan duk wani abun da aka saya a nan na taimakawa matalauta samun karin kudin shiga.

Yayin da sayayyar da jama'a suke yi ke haifar da riba ga masana'antu, a nasu bangare, wasu kamfanoni su ma sun fara taka muhimmiyar rawa a kokarin kau da talauci a kasar Sin. Nie Wei, shi ne shugaban rumfar Xinjiang dake cikin kasuwar. A cewarsa, kamfaninsa ya kan dauki matalauta aiki a matsayin ma'aikatansu, gami da sayen dabinon da manoma masu fama da talauci suka samar. Ta wannan hanya sun taimakawa magidanta 1200 na gundumar Hotan ta jihar Xinjiang fitowa daga kangin talauci. A sa'i daya kuma, manufar kau da talauci na taimakawa kamfaninsu samar da karin kayayyaki. Nie ya ce,

"Dabinon jihar Xinjiang na da dadi. Sai dai a can baya ba mu da damar shigar da dabinonmu cikin kasuwannin Beijing. Daga bisani manufar tallafawa yankuna masu fama da talauci ta sa mu samun damammakin sayar da kayayyakinmu a Beijing. Yanzu yawan kayan da muke sayarwa ya ninka sau daya."

Wasu wuraren kasar Sin na fama da talauci ne sakamakon rashin wata sana'ar dake iya samar da dimbin kayayyaki masu inganci. Saboda haka, wasu kamfanoni suna kokarin taimakawa wadannan wurare raya wasu sana'o'i. Li Zhaolong, shi ne mai kula da rumfar wani kamfanin dake lardin Qinghai dake yammacin kasar Sin, wanda ya gaya mana cewa,

"Mun yi kokarin neman wasu kayayyakin da za su biya bukatar kasuwa. An samar da kayayyakin ne cikin kananan wuraren aiki, don haka mun taimaka musu tabbatar da ingancin kayayyakin, ta yadda zai dace da ma'auni na kasuwannin Beijing. Ta wannan hanya, muna taimaka musu raya wasu sana'o'i."

A wannan kasuwar ta tallafawa matalauta, ban da kamfanoni dake kokarin taimakawa matalauta, har ma akwai wasu talakawan da ke neman sayar da kayayyakinsu. Madam Liu Xiaoling tana kokarin gabatar da wasu kayayyakin al'adun gargajiya da mutanen kauyenta suka samar. A cewarta, a baya ita da 'ya'yan ta biyu suna dogaro kan mijinsa wajen samun kudin sayen abinci, domin shi kadai yana aiki a lokacin. Amma daga bisani, ta halarci kwas na koyon fasahar samar da kayayyakin al'adu, ta yadda yanzu ta iya tsara kayayyakin, da kuma sayar da su don samun karin kudin shiga. A yanzu haka kawai bukatar sayar da karin kayayyakin da suka samar. A cewar ta,

"Yanzu odar kayayyakin da muka samu ba yawa. Wani lokaci ma sai an yi jira har wasu watanni 6 kafin a samu wata oda. Don haka dole ne a yi kokarin sayar da karin kaya."

An ce ko da bikin bazara na wannan shekara ya kammala, ba za a rufe kasuwar nan ta tallafawa matalauta ba, ta yadda kasuwar za ta ci gaba da taka rawa a kokarin da ake na kau da talauci gaba daya daga kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China