Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: An daura aure sama da miliyan tara a bara
2020-01-20 09:51:35        cri
Ma'aikatar lura da al'amuran al'umma ta kasar Sin, ta ce yawan ma'aurata da suka yi rajista domin kulla aure tsakaninsu a shekarar 2019 ya haura miliyan 9.47, ko da yake wannan adadi bai kai miliyan 10.1 da aka samu a shekarar 2018 ba. A daya hannun kuma an yi rajistar kisan aure kusan miliyan 4.15 a shekarar ta 2019.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Lahadi a nan birnin Beijing, jami'i a ma'aikatar Yang Zongtao, ya ce yawan auratayya a kasar Sin na raguwa tun daga shekarar 2014, sakamakon raguwar hayayyafa wadda ta biyo bayan aiwatar da dokar kayyade iyali ta shekaraun 1970 da 1980. Ya ce sauyin mahanga game da aure, ya yi tasiri ga raguwar masu niyyar yin aure.

Yang ya kara da cewa, ma'aikatar za ta samar da rumbun bayanai na kasa, wanda zai tattara bayanai game da lamuni domin aure, da aiwatar da matakan dakile almubazzanci yayin bukukuwan aure, da nufin dakile almundahana mai nasaba da harkar aure a kasa baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China